Connect with us

Featured

Duk da Samun Ƙaruwa da Gwamnati Ta Ke Yi a Ɓangaren Haraji Hakan Ba Zai Sa a Daina Ciyo Bashi Ba – FIRS

Shugaban Hukumar Haraji na Ƙasa (FIRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa duk da ƙaruwa da aka samu a bangaren harajin cikin gida, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da karɓo rance domin cike gibi a kasafin kuɗi da kuma aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa. Adedeji ya yi wannan bayani ne a Aso Villa, Abuja, yayin taron manema labarai na Meet-the-Press da Ƙungiyar Yaɗa Labaran Fadar Shugaban Ƙasa ta shirya.

Ya ce gwamnati ta tara haraji mai tsoka na N3.64 tiriliyan a watan Satumba 2025 – ƙaruwa da kashi 411% daga N711 biliyan da aka tara a watan Mayu 2023. Hukumar ta ce wannan ci gaban ya samo asali ne daga karuwar kudaden shiga da aka samu, inda aka tara N1.06 tiriliyan daga N151 biliyan a bara; kudaden shiga daga mai sun kai N644 biliyan, yayin da VAT ya ninka fiye da sau uku zuwa N723 biliyan.

Adedeji ya kare tsarin ciyo bashi da gwamnati ke yi, yana mai cewa ba wata ƙasa ko kamfani da ke bunƙasa ba tare da rance ba. Ya bayyana cewa rance ba don biyan albashi ake ɗauka ba, sai dai don gina muhimman ayyuka kamar hanyoyi da ke amfani ga al’ummar yanzu da na gaba.

Shugaban FIRS ya ce tsarin gwamnati na yanzu ya haɗa da sauƙaƙa haraji, rage nauyi ga ƙananan kasuwanni, da kuma haɗa haraji na jihohi domin ƙarfafa biyan kuɗi. Ya kuma ce za a ƙaddamar da sabon tsarin haraji, da rage harajin kamfanoni, domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. A cewarsa, waɗanda ke sukar rance na gwamnati ba sa fahimtar asalin lamarin, suna takaita bayanansu ne daga hayaniyar kafafen sada zumunta ba tare da sanin tsarin tattalin arziki na ƙasa ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet