Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Canzawa Hukumar FIRS Suna Zuwa NRS – Zacch Adedeji
Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta sanar da shirin canza sunanta zuwa Nigeria Revenue Service (NRS) daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Shugaban hukumar, Dakta Zacch Adedeji, ne ya bayyana haka, yana mai cewa wannan mataki wani muhimmin ɓangare ne na shirin gwamnati na gyaran tsarin tattalin arziki da samar da ingantaccen tsarin tara kuɗaɗen shiga na ƙasa. Ya ce sabon tsarin zai faɗaɗa ikon hukumar, domin ta fara karɓar kuɗaɗen da ba haraji ba daga Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Sama (NUPRC), tare da tabbatar da gaskiya da inganci wajen tara kudaden gwamnati.
Adedeji ya bayyana cewa wannan sauyi zai zama jigo wajen kawo sabuwar hanya ta gudanar da haraji ta zamani, wadda ke amfani da fasahar zamani da tsarin dijital domin rage wahalar biyan haraji da hana ɓata lokaci. Ya ce a karkashin sabon tsarin, hukumar za ta ci gaba da inganta ayyukanta ta hanyar National Single Window Project da tsarin e-invoicing, wanda ke haɗa hukumomin gwamnati da ‘yan kasuwa domin tabbatar da sauƙin mu’amala da bin doka.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa, tun bayan hawansa kan mulki, FIRS ta samu gagarumar nasara wajen tara kuɗaɗe, inda ta tattara Naira tiriliyan 22.59 a cikin wata tara na shekarar 2025, da kuma jimillar Naira tiriliyan 47.39 cikin shekara guda. Ya ce wannan ci gaban ya nuna cewa sauye-sauyen da ake yi a hukumar suna ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasa, musamman ta fuskar samun kudaden da ba na mai ba, wanda ya kai kashi 76 cikin 100 na dukkan kudaden da aka tara.
A ƙarshe, Adedeji ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da sabbin dokokin haraji cikin gaskiya da daidaito, tare da horar da jami’ai da wayar da kan ‘yan kasuwa. Ya ce manufar canjin suna zuwa NRS ita ce samar da sabuwar hukumar da ke wakiltar zamani, fasaha, da sauƙin biyan haraji — domin tabbatar da cewa kudaden shiga na ƙasa suna gudana cikin tsari, gaskiya da kuma amfanin al’umma baki ɗaya.
