Connect with us

Featured

Gwamnatin Mali Ta Rufe Makarantu Na Tsawon Makonni Biyu Saboda Ƙarancin Man Fetur

Gwamnatin ƙasar Mali ta sanar da rufe dukkanin makarantu da jami’o’i a fadin ƙasar na tsawon mako biyu sakamakon matsalar karancin man fetur da ake fama da shi. Rahotanni sun bayyana cewa wannan matsalar ta samo asali ne bayan da mayakan ƙungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) suka kafa takunkumi kan shigo da man fetur tun farkon watan Satumba.

An ce mayakan sun yi nufin toshe hanyoyin tattalin arzikin ƙasar domin matsa lamba ga gwamnatin soji ta Mali. Tun bayan fara wannan takunkumi, an samu rahotannin kai hare-hare kan motocin daukar mai da ke ƙoƙarin shiga birnin Bamako, abin da ya janyo rufe gidajen mai da dama, tare da tilasta wa mazauna yin tafiya a ƙafa ko amfani da babura masu haya.

A wani mataki na tallafawa ƙasar, Rasha ta sanar da shirinta na turo tan dubu 160 zuwa 200 na kayan mai da amfanin gona zuwa Mali domin rage radadin matsalar. Wakilin Rasha, Alexey Keulika, ya ce za a gudanar da wani taro a watan Nuwamba kan sabon kamfanin tace zinari wanda Rasha ke tallafawa gina shi a ƙasar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Mali ke fuskantar tsaikon karatun makarantu ba, domin a shekarar 2024 ma an jinkirta fara zangon karatu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta shafi sassan ƙasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet