Featured
NEMA Ta Karɓi Ƴan Najeriya 145 da Aka Kwaso Daga Algeria
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa ta karɓi ‘yan Najeriya 145 da aka kwaso daga Aljeriya bayan sun maƙale a ƙasar. Hukumar ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas da misalin ƙarfe 12:15 na rana a ranar Litinin, ta jirgin Air Algeria.
A cewar NEMA, waɗanda aka dawo da su sun haɗa da maza manya 132, yara tara da kuma jarirai huɗu. Hukumar ta ce ƙungiyar kula da ‘yan ci-rani ta duniya, wato International Organization for Migration (IOM), ce ta ɗauki nauyin kwaso mutanen tare da haɗin gwiwar gwamnatin Najeriya.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka kwaso wasu ‘yan Najeriya 148 daga Sudan a ranar Alhamis da ta gabata, bisa irin wannan shirin na haɗin gwiwa. NEMA ta ce shirye-shiryen karɓar ‘yan Najeriya da suka makale a ƙasashen waje na ci gaba a ƙasar.
Hukumar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje da su yi taka-tsantsan wajen yin hijira ba bisa ka’ida ba, tana mai jaddada cewa gwamnati da abokan hulɗarta na ci gaba da ƙoƙari don dawo da ‘yan ƙasar cikin mutunci da aminci.
