Connect with us

Featured

Daga Yanzu Sai Ɗalibi Ya Kawo Project Ɗinsa Sannan Zai Tafi NYSC – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar doka wadda ta wajabta cewa duk ɗaliban da suka kammala karatun jami’a ko kwalejin koyarwa – a gida ko ƙasashen waje – sai sun miƙa takardun binciken kammala karatu (thesis) ko aikin ƙarshe na shekara zuwa Nigeria Education Repository and Databank (NERD) kafin a yi musu rajistar shiga hidimar National Youth Service Corps (NYSC). Wannan doka za ta fara aiki daga 6 ga Oktoba, 2025.

Wannan mataki ya fito ne ta wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya aika, inda ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da wannan sabon tsarin. Doka ta ce babu ɗalibi da zai shiga NYSC ba tare da ya gabatar da hujjar ya bi wannan ka’ida ba.

NERD ta bayyana manufar wannan mataki a matsayin tsari na tabbatar da inganci da sahihancin rubuce-rubucen dalibai, tare da sa ido kan ci gaban ayyukan bincike a duk fadin ƙasar. A cikin bayanin ta, kakakin hukumar, Haula Galadima, ta ce shirin zai ɗorawa manyan malamai alhakin kulawa da ingancin rubuce-rubucen ɗaliban da suke jagoranta domin sun san sunayensu za su bayyana a fili a wannan dandali na intanet.

Haka kuma, dokar ta NERD za ta tabbatar da adana cikakken bayani game da aikin kammala karatun dalibai da sunan ɗalibin, sunan mai kula da shi, shugaban sashen karatunsa da makarantar da ya fito. A cewar Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, shirin ya kuma ƙunshi tsarin ba da lada ga dalibai da malamai bisa ga ingancin ayyukansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet