Connect with us

Featured

Jami’o’in Benin Da Wasu Kwalejin Fasaha a Najeriya Na Yunƙurin Shigar Da Ɗalibansu Tsarin NYSC Ta Ɓarauniyar Hanya

Binciken jaridar Saturday PUNCH ya gano cewa wasu jami’o’i da gwamnatin Najeriya ta haramta a Jamhuriyar Benin sun ƙirƙiro wata dabara ta shigar da ɗalibansu cikin shirin bautar ƙasa (NYSC) ta hanyar haɗin gwiwa da wasu makarantun kwalejin fasaha masu zaman kansu a Najeriya. Jami’o’in da aka haramta yanzu suna samun takardun National Diploma (ND) da Higher National Diploma (HND) daga waɗannan makarantu na kimiyya da fasaha domin ba da damar ɗalibansu su shiga tsarin NYSC. Rahotanni sun nuna cewa dalibai suna biyan kusan N400,000 domin samun takardun HND daga makarantun kimiyyanda fasaha da ke yankin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas. Wannan ya biyo bayan dakatarwar da gwamnati ta yi a 2024 daga tantancewa da amincewa da takardun digiri daga jami’o’in Benin da Togo bayan an gano hanyar da ake samun takardar digiri cikin makonni kaɗan.

Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun tabbatar da wannan tsarin. Seun, wani ɗalibi daga Esfam-Benin University da ke cikin jerin jami’o’in da aka haramta, ya ce an riga an tura bayanansa zuwa wata makarantar polytechnic a Najeriya domin shirye-shiryen shiga NYSC. Ya bayyana cewa wasu daga cikin abokan karatunsa sun riga sun samu takardun HND kuma suna jiran kira daga NYSC. Wani dalibi, Isa, ya tabbatar da cewa an shirya masa shiga bautar ƙasa ta hanyar wata makarantar kimiyya da fasaha (Polytechnic) a Jihar Abia, inda ya samu takardun ND da HND. Haka kuma, wasu jami’an jami’o’i a Benin sun bayyana yadda tsarin ke tafiya — daga fitar da takardar digiri, zuwa haɗa sunayen ɗalibai a “senate list” na polytechnic, sannan a karɓi kuɗaɗe kafin a kammala shiryawa da fitar da takardun bogi.

Wasu daga cikin iyalai ma sun tabbatar da biyan kuɗi domin shigar da ‘ya’yansu cikin wannan tsarin. Wunmi, wata mata da dan uwanta ya kammala karatu a Benin, ta bayyana cewa ta biya N500,000 ga wata makarantar polytechnic a Jihar Ekiti domin tabbatar da shiga NYSC. Bincike ya kuma gano takardun da aka ƙirƙira, inda aka samar da lambar shiga makaranta, CGPA, da sakamakon ND/HND na bogi ga wasu dalibai daga jami’o’in Benin. Sai dai wani jami’i daga Esfam-Benin University ya musanta cewa makarantar su na da hannu a irin wannan harkalla, yana mai cewa suna jiran matakin karshe daga gwamnati kan batun dakatar da jami’o’in Benin da Togo.

A nasa bangare, hukumar NYSC ta ce ba ta da masaniya game da irin wannan tsarin, inda ta bayyana cewa dukkan ɗaliban kasashen waje suna wucewa ta ma’aikatar ilimi kafin a tantance su. Haka kuma, ma’aikatar ilimi ta Najeriya ta ce ba zai yiwu a yi wannan damfara ba saboda an ƙirƙiro tsarin dijital don hana irin wannan kutse. Haka zalika, shugaban ƙungiyar shugabannin polytechnics da kwalejojin fasaha na Najeriya, Dr. Usman Tunga, ya ce bai da masaniya game da irin wannan abu, amma ya tabbatar da cewa idan an gano wata makaranta na aikata hakan, za a kai rahoto ga hukumomin da suka dace don ɗaukar mataki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetpusulabetvdcasinograndpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetcasibom girişcasinolevantcasinolevantsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetcasibommatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet