Connect with us

Addini

Majalisar Ƙoli Ta Addinin Musulunci Ta Musanta Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta karyata zargin da wasu kafafen yada labarai na waje da masu amfani da kafafen sada zumunta suka yada cewa ana gudanar da kisan gilla kan Kiristoci a Najeriya. Majalisar ta bayyana cewa wannan zargi karya ne, haɗari ne ga zaman lafiya, kuma an kitsa shi ne domin tayar da hankali da rarrabuwar kawuna a ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan wani Sanatan Amurka, Ted Cruz, ya zargi gwamnatin Najeriya da shirya kisan kiyashi kan Kiristoci, yana mai cewa sama da Kiristoci 52,000 ne aka kashe tun daga 2009, tare da rushe majami’u da makarantu fiye da 20,000. Haka kuma, ya gabatar da kudirin dokar “Nigeria Religious Freedom Accountability Act” a Majalisar Dattawan Amurka domin kakabawa jami’an Najeriya takunkumi.

A wata sanarwa da Majalisar ƙolin ta fitar ta hannun Mataimakin Mai Ba da Shawara na Harkokin Shari’a na ƙasa, Imam Eze, ranar 10 ga Oktoba, 2025, majalisar ta ce rahotannin da ke zargin gwamnatin tarayya da hannu wajen kashe Kiristoci ba su da hujja kuma ɓatanci ne ga Najeriya. Ta bayyana cewa wasu ‘yan Najeriya — da ta kira “wakilan CAN” — ne ke yada wannan labari a waje domin neman tallafi da ƙarfafa matsayinsu ta hanyar bata sunan ƙasar. Majalisar ta gode wa hukumomi da mutane da suka yi gaggawar karyata zargin, tana mai kira ga gwamnati ta fallasa waɗanda ke yada irin waɗannan labarai.

NSCIA ta kuma jaddada cewa babu wani hujja da ke nuna cewa ‘yan ta’adda suna kai hare-hare ne musamman kan Kiristoci. Ta ce rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na 2023 ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu laifi suna kai hare-hare kan masallatai da majami’u ba tare da bambanci ba. A cikin rabin farko na 2025 kadai, rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane fiye da 2,200 a Arewa, inda Musulmi suka fi rinjaye, kuma sama da mutane miliyan biyu sun rasa matsugunnai. Majalisar ta zargi wasu manyan shugabannin Kirista da yaɗa “ƙarya mai muni” domin samun goyon bayan ƙasashen waje, tana ambaton Bishop Wilfred Chikpa Anagbe da Rev. Joseph Hayab a matsayin misalai.

Bugu da ƙari, Majalisar ta soki wasu matakan gwamnati da ta ce na iya ƙara rarrabuwar kawuna, kamar yadda ta nuna rashin amincewa da wata doka daga Hukumar Inshora ta Ƙasa (NAICOM) da ta hana haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin inshora na al’ada da na Takaful. Duk da haka, NSCIA ta jaddada cewa tana goyon bayan Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya mai haɗin kai, kuma za ta ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai, duk da ƙalubale da tada jijiyar wuya daga wasu ɓangarori.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet