Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba 1 Ga Oktoba a Matsayin Ranar Hutu a Fadin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da sakatariyar dindindin ta ma’aikatar, Dokta Magdalene Ajani ta sanya hannu a ranar Litinin 29 ga Satumba.

A cewar sanarwar, Ministan ya taya ‘yan Najeriya murna, a gida da waje, yana kuma kira ga al’umma su ci gaba da rike darajar kishin kasa, hadin kai da juriya da suka taimaka wajen dorewar kasar tun bayan samun ‘yanci a 1960. Ya kuma bukaci ‘yan kasa su ba da goyon baya ga shirin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu da ya mayar da hankali kan sake gina kasa, habaka tattalin arziki da wadata tare.

Tunji-Ojo ya bayyana tabbacin cewa tare da hadin kan al’umma, Najeriya za ta ci gaba da kara karfi a bangaren zaman lafiya, ci gaba da cigaban tattalin arziki. Ya yi kira ga kowa da kowa ya rungumi wannan dama domin ciyar da kasa gaba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantpusulabetvdcasinograndpashabetmarsbahisholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişcasibompusulabetpusulabetmatadorbetonwinimajbetmatbetmatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantcasinolevantsahabetsekabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet