Featured
ASUU Ta Baiwa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Ko Ta Tsunduma Yajin Aiki
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14 domin ta warware matsalolin da suka dade suna jawo rikici a tsakanin ɓangarorin biyu. Kungiyar ta yanke wannan matsaya ne bayan taron majalisar zartarwarta ta ƙasa (NEC) da aka gudanar a Jami’ar Abuja a ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025. Kamar yadda Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya sanar da hakan a Abuja.
ASUU ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da al’amuran jami’o’i tare da yin biris da buƙatun da kungiyar ke gabatarwa tun daɗewa. Kungiyar ta ce idan aka ƙi ɗaukar mataki cikin wa’adin kwana 14 da aka bayar, za ta fara yajin aikin gargadi na mako biyu sannan daga bisani ta shiga yajin aiki gaba ɗaya ba tare da iyaka ba.
Tun da farko, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kafa kwamitin da babban sakatare na ma’aikatar, Abel Enitan, ke jagoranta domin nazarin shawarwarin ASUU da nufin samar da zaman lafiya a jami’o’i. Sai dai har zuwa yanzu, ba a bayyana sakamakon tattaunawar kwamitin ga jama’a ba.
A cewar ASUU, bukatunsu na asali ba su canja ba: sake duba yarjejeniyar 2009, samar da isasshen kudin farfaɗo da jami’o’i, biyan bashin albashin da ake binsu, da samar da ingantaccen tsarin kudade na dorewar jami’o’i a Najeriya.
