Featured
Magance Matsalar Talauci Da Cutar Maleriya Zai Dauki Tsahon Lokaci a Najeriya – Gidauniyar Bill Gate
Shugaban Bill & Melinda Gates Foundation, Mark Suzman, ya bayyana cewa yaƙar talauci da cutar maleriya a Najeriya zai ɗauki shekaru masu yawa kafin a samu gagarumar nasara. Ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi wajen inganta kiwon lafiya, girman ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta na nufin cewa aikin ba zai yiwu a ɗan gajeren lokaci ba.
Suzman, wanda ya yi wannan bayani a New York, ya jaddada cewa Najeriya na taka muhimmiyar rawa a kididdigar Afirka da duniya baki ɗaya. Ya ce akwai mutane dayawa da ke rayuwa a ƙasa da dala biyu a rana a Najeriya, fiye da kowace ƙasa a duniya, haka kuma akwai matsalolin yawan yara da ba a yi wa allurar rigakafi ba da kuma yawaitar kamuwa da maleriya.
Ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu muhimman matakai, musamman ta hannun Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, wanda ya sa batutuwan rigakafi da yaƙi da maleriya a gaba. Sai dai ya ce gagarumar nasarar da za a samu za ta bayyana ne a nan gaba idan aka samu ƙarni na matasa da suka taso cikin koshin lafiya da ingantaccen abinci.
Suzman ya ƙara da cewa nasarorin yaƙi da cututtuka kamar maleriya kan haifar da ci gaban tattalin arziƙi na dogon lokaci, ba nan da nan ba. Ya ce Najeriya na ƙoƙarin bunƙasa kuɗaɗen haraji domin rage dogaro da man fetur, amma ƙalubale na tattalin arziƙi da na kuɗi na ci gaba da kasancewa babbar barazana.
