Connect with us

Featured

Masu Karuwanci Za Su Fara Biyan Haraji a Najeriya – Gwamnatin Tarayya

Shugaban Kwamiti kan Sauye-Sauyen Haraji, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa duk wani kuɗin shiga da ake samu a Najeriya – ko da daga sana’a ce ta halas ko ta haram – ana ɗaukar sa a matsayin abin da ya kamata a biya haraji. Ya ce idan mutum ya ba wani kyauta ko kuɗin kulawa, ba a ɗora masa haraji, amma duk inda aka biya kuɗi kan wani aiki ko hidima, wajibi ne a biya haraji.

A wani taron wayar da kan jama’a da aka shirya a RCCG City of David, Lagos, Oyedele ya bada misali da masu yin karuwanci da ake kira runs girls, inda ya ce duk kuɗin da suka samu daga yin lalata da maza ana ɗaukar shi a matsayin kuɗin shiga, don haka dokar haraji tana buƙatar su biya. Ya jaddada cewa dokar haraji ba ta bambance tsakanin halal da haram wajen samun kuɗi, illa kawai tana tambaya: “Ka samu kuɗi ne daga aiki ko samfur? To sai ka biya haraji.”

Sai dai ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci manufar gaba ɗaya ta sabon tsarin haraji, maimakon su mai da hankali ga bangare guda. Ya kwatanta hakan da tatsuniyar makaho da giwa, inda kowa ya tabo wani ɓangare daban-daban amma babu wanda ya gane hakikanin abin da giwar take.

An bayyana cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, kuma su ne mafi girma a tarihin Najeriya. Sabbin dokokin sun haɗa da ƙa’idoji fiye da 200, suna kuma sassauta haraji ga ma’aikatan da ba su kai samun N800,000 a shekara ba, da ƙananan kamfanoni da ke da juyin kuɗi ƙasa da N100m da kadarori ƙasa da N250m. Gwamnati na sa ran wannan sauyi zai sauƙaƙa tsarin biyan haraji da kuma hana rikice-rikice kan haraji mai yawa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet