Featured
Gwamnan Kogi Ya Bayar Da Umarnin Rufe Garejin Manyan Motoci a Jihar
Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo, ya bayar da umarnin rufe garejin manyan motoci da ake amfani da su ba bisa ka’ida ba a Zariagi da ke Lokoja da kuma Osara a karamar hukumar Adavi. Gwamnan ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar a Lokoja, inda ya ce rufe wuraren na tsawon wata guda ya zama dole saboda rahotannin tsaro da ke nuna cewa wuraren na zama mafakar masu laifi da ke fakewa da sunan direbobin manyan motoci.
Ododo ya jaddada cewa lafiyar al’umma da tsaron jihar Kogi su ne ginshiƙan ci gaba, don haka bai kamata a ba wa ’yan ta’adda damar samun mafaka ba. Ya ce an ba wa masu amfani da garejin wata guda kacal domin su fice daga wuraren da aka hana amfani da su, musamman a lokutan da aka sanya dokar hana zirga-zirga. Ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da bin wannan doka ba tare da sassauci ba.
A cewarsa, wannan mataki na cikin kokarin tabbatar da cewa Kogi ta kasance jiha mai tsaro, inda kowane ɗan ƙasa zai samu damar rayuwa cikin kwanciyar hankali.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali sakamakon hare-haren ’yan bindiga a jihar. A farkon wannan watan, wasu ’yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda uku da kuma mambobin sa-kai biyu a wani shingen bincike a garin Egbe, karamar hukumar Yagba West. Wannan lamarin ya ƙara tayar da hankalin jama’a tare da nuna ƙalubalen da hukumomin tsaro ke fuskanta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
