Connect with us

Featured

Kotu Ta Dakatar Da Ƴan Sanda Daga Aiwatar Da Dokar Tilasta Mallakar Lasisin Baƙin Gilashin Mota

Babbar Kotun Tarayya da ke Warri, Jihar Delta, ta ba da umarnin dakatar da rundunar ‘yan sandan Najeriya da Sufeto Janar na ‘yan sanda daga aiwatar da tilasta wa direbobi samun lasisin gilashin mota mai duhu (tinted glass permit). Wannan umarni ya biyo bayan buƙatar da lauya John Aikpokpo-Martins ya shigar a gaban kotu, inda ya kalubalanci sahihancin wannan sabuwar doka ta tilasta lasisin.

Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi ga ‘yan sanda da Sufeto Janar su ci gaba da bin tsarin doka tare da mutunta shari’a, har sai an kammala sauraron ƙarar. Wannan umarni yana cikin shari’a mai lamba FHC/WR/CS/103/2025, wadda ake ci gaba da sauraro a gaban kotun.

Lauyan ya bayyana cewa wannan doka ta tilasta lasisin ba ta da tushe a tsarin mulki, don haka ya nemi kotu ta dakatar da aiwatar da ita har sai an yanke hukunci. Lauyan ya ce matakin ya zama wajibi domin kare ‘yancin direbobi daga cin zarafi da kuma aiwatar da abin da bai dace ba.

Babban Lauya (SAN) Kunle Edun, wanda ya jagoranci tawagar shari’a ta mai ƙara, ya tabbatar da wannan ci gaban ga manema labarai. Ya bayyana cewa wannan umarni babbar nasara ce ga tsarin mulki da mulkin doka, domin yana tabbatar da cewa ‘yan sanda ba za su ci gaba da aiwatar da abin da ke gaban kotu ba, har sai an yanke hukunci kan batun gaba ɗaya.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet