Connect with us

Featured

Sojoji 16 Za Su Fuskanci Shari’a Sakamakon Karya Ƙa’idojin Aiki — Hedikwatar Tsaro Ta Ƙasa

Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa an kama jami’an soja 16 da ake zargi da aikata laifukan rashin ladabi da karya ƙa’idojin aikin soja, kuma za su fuskanci shari’ar ladabtarwa. Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 04 ga Oktoba, inda ya ce an gano laifukan ne yayin wani binciken yau da kullum da rundunar soji ta gudanar.

Gusau ya bayyana cewa bincike ya nuna yawancin matsalolin jami’an sun samo asali ne daga rashin gamsuwa da cigaban aikinsu, musamman gazawar da suka sha fuskanta a jarrabawar ƙarin matsayi. Wasu daga cikin jami’an da aka kama ma tun da farko suna ƙarƙashin bincike ko shari’a kan wasu laifuka daban-daban.

Ya ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifi a gaban kotun soja domin fuskantar cikakken tsarin ladabtarwa da doka ta tanada. Wannan mataki, a cewarsa, yana da nufin tabbatar da gaskiya, ɗa’a, da kiyaye kwarewar aiki a cikin rundunar sojin Najeriya.

Gusau ya jaddada cewa rundunar sojin ba za ta lamunci duk wani hali da zai lalata martabar soji ko ya kawo barazana ga rawar da rundunar ke takawa a tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba. Ya ƙara da cewa rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da aiwatar da aikinta bisa ƙwarewa da bin ƙa’ida a kowane lokaci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet