Connect with us

Featured

Ƴan Bindiga Sun Sace Hakimi a Kwara

Wasu ’yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara, inda suka harbe wani mutum har lahira tare da yin garkuwa da basaraken ƙauyen, Alhaji Ndako. Lamarin ya faru ne a yayin da ake cikin Sallar Magariba ranar Lahadi 05 ga Oktoba, lokacin da maharan suka kutsa cikin ƙauyen a kan babura, suna harbe-harbe ba tare da tsoro ba.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji tare da basaraken da suka sace. A cewar mazauna yankin, mutanen ƙauyen sun shiga ruɗani da gudu domin tsira da rayukansu, inda a wannan hali ne maharan suka harbi ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen har lahira.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Patigi, Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mafarauta da ’yan banga sun bi sawun maharan domin ceto hakimin. Ya bayyana cewa hukumar ƙaramar jihar tare da jami’an tsaro da ’yan banga na aiki kafada da kafada don magance matsalar tsaro a yankin. Ya kuma jaddada buƙatar fatattakar miyagu daga dazukan yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Harin ya faru ne yayin da gwamnatin jihar ta ke ƙoƙarin inganta tsaro, inda Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya gudanar da taro tare da masu ruwa da tsaki na ƙananan hukumomin Patigi da Edu. Inda aka tattauna hanyoyin tabbatar da tsaro da kuma shirin ɗaukar jami’an tsaron dazuka tare da samar musu da kayan aiki don magance barazanar ’yan bindiga a yankin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino sitelerikavbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwingrandpashabet güncel girişjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetgrandpashabet güncel girişcasinolevantbetgarantibetciograndpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabet girişpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet