Featured
Mutum 38 Da Aka Sace a Cocin Kwara Sun Shaƙi Iskar Ƴanci
Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da cewa mutane 38 da ‘yan bindiga suka sace a cikin cocin Christ Apostolic Church (CAC) na Eruku, Karamar Hukumar Ekiti, sun samu ‘yanci bayan kwanaki da dama ana gudanar da bincike da aiki tare tsakanin jami’an tsaro. Sanarwar, wadda ta fito daga ofishin mai magana da yawun gwamnan jihar, Rafiu Ajakaye, ta ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar kubutar da mutanen.
A cewar gwamnan, wannan nasara ta samu ne saboda kulawar kai tsaye da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wajen ganin an ceto wadanda aka sace. Tinubu ya dage tafiyarsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu domin ba da umarnin ƙarin jami’an tsaro da kuma jagorantar matakan da suka tabbatar da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
A yayin da take bibiyar lamarin, Kakaki24 ta tattaro cewa gwamnatin tarayya, ta hannun NSA, DSS, Sojoji, Hukumar Leken Asiri (NIA), da ‘Yan Sanda, sun tura ƙungiyoyi na musamman hudu zuwa Kwara domin kakkabe maboyar ‘yan bindiga. Jami’an cocin CAC Oke Isegun sun tabbatar da cewa DSS ta sanar da su kusan ƙarfe 4 na yamma cewa mutanen sun kubuta kuma ana shirin dawo da su cikin al’umma domin saduwa da iyalansu.
Lamarin sace mutanen 38 da kashe wasu uku a lokacin hari ya haifar da firgici da cece-kuce a fadin ƙasar, kasancewar daya ne daga cikin manyan hare-haren da aka yi a Kwara kwanan nan. Sai dai hukumar tsaro da jami’an sa-kai sun gudanar da aikin bincike mai zurfi wanda ya kai ga kubutar da mutanen cikin koshin lafiya.
