Featured
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Bauchi Ta Rufe Dukkan Makarantu a Fadin Jihar
24 ga Nuwamba 2025 | Lahadi
Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu a fadin jihar saboda tsananin tashin hankalin tsaro da ya yi kamari a yankin. Sanarwar, wacce ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa matakin ya zama wajibi domin kare rayukan dalibai, malamai da sauran ma’aikata a makarantun jihar.
A cewar mai magana da yawun ma’aikatar, Jalaludeen Usman, an dauki wannan mataki ne bayan shawarwari masu zurfi tare da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki. Ya ce gwamnati ta san takura da wannan mataki zai kawo ga iyaye da dalibai, amma daukar wannan mataki ya zama wajibi, musamman ganin yadda hare-haren sace dalibai suka karu a jihohin Kebbi da Neja a kwanakin baya.
A cikin rahotonmu na Kakaki24, mun gano cewa fargaba ta karu a sassan Arewa bayan bullar sabbin hare-haren da ake kaiwa makarantu, lamarin da ya sa hukumomi a jihohi daban-daban ke daukar matakan gaggawa domin kaucewa abin da ka iya faruwa. Wannan mataki na Bauchi ya biyo bayan matakin gwamnatin tarayya na rufe wasu makarantun unity 41 saboda irin wadannan barazanar tsaro.
Gwamnatin Bauchi ta yi kira ga iyaye, shugabannin makarantu da al’umma su kwantar da hankalinsu tare da taimakawa hukumomin tsaro da bayanai idan sun ga wani abin da bai dace ba. Ta ce za a cigaba da sabunta bayanai kan yanayin tsaron, tare da fatan komawa karatu da zarar an tabbatar da tsaro.
