Featured
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Ƙwace Fasfo Na Tsawon Shekara 10 Ga Duk Wanda Aka Samu Da Aikata Laifuka a Ƙetare
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da sabuwar doka da ta haramta wa duk wani ɗan ƙasa da aka samu da aikata laifi a ƙasashen waje yin amfani da fasfon Najeriya na tsawon shekara 10. An cimma wannan matsaya ne a yayin zaman majalisar da aka gudanar a Abuja, ranar Talata 07 ga Oktoba, 2025.
Sanata Abubakar Bello mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya gabatar da ƙudurin a gaban majalisar, a wani bangare na gyara dokar da ta shafi fasfo. Ya bayyana cewa matakin zai zama hanya ta hukunta ƴan ƙasar da ke aikata manyan laifuka a waje tare da ƙarfafa ladabtarwa.
Ƙudurin ya tanadi cewa a karɓe fasfo na tsawon shekara 10 mafi ƙaranci daga hannun duk wanda aka tabbatar da laifinsa a ƙetare. Majalisar ta bayyana cewa wannan zai zama darasi ga wasu da ke lalata suna da mutuncin ƙasar a idon duniya.
Ƴan majalisar sun nuna kwarin gwiwa cewa matakin zai taimaka wajen magance matsalar ɓata sunan ƙasar, tare da inganta martabar Najeriya a ƙasashen waje.
