Featured
Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Buƙaci a Dakatar da Yakin-Neman-Zaɓe a Jihohi 8 Na Arewa
Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan gaggawa kan matsalar tsaro, ciki har da yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a wasu jihohin arewa guda takwas da rikici ya fi kamari.
Bukatar ta biyo bayan wani ƙuduri da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya gabatar a zauren majalisar, inda ya bayyana cewa ya zama dole a dakatar da harkokin siyasa a jihohin Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi da wasu sassan Kano har sai an samu sauƙin matsalar tsaro.
Majalisar ta kuma yi Allah wadai da hare-haren ‘yan Boko Haram kan sansanonin sojoji, tare da kira ga gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen ceto mutane 416 da aka sace a Borno, yayin da ta bukaci rundunar soji ta binciki matsalolin kayan aiki da dabarun yaki domin shawo kan barazanar tsaro.
