Featured
Ƴan Sanda Sun Cafke Mutanen Da Ake Zargi Da Kisan Ƴar Jaridar Arise TV a Abuja
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa ta kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kisan ‘yar jaridar gidan talabijin na Arise TV, Somtochukwu Maduagwu, wadda aka fi sani da Sommie. Wannan na zuwa ne kwanaki 10 bayan ta rasa ranta a wani mummunan hari da ‘yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe, Abuja. Lamarin ya faru ne da tsakar dare a ranar 29 ga watan Satumba, inda maharan suka kutsa cikin gidan suka kasheta.
Baya ga Sommie, wani mai gadin gidan mai suna Barnabas Danlami shima ya mutu yayin fashin. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga ne da niyyar fashi, sai suka hallaka mutanen biyu a lokacin harin. Wannan lamari ya tayar da hankalin al’umma.
A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sanda ta fitar ranar Alhamis 09 ga Oktoba, ta ce waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu bayan an kama su. Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa an cafke huɗu daga cikinsu ne jim kaɗan bayan faruwar lamarin ta hanyar bin diddigin wayoyinsu na salula, wanda hakan ya kai ga kama sauran.
Sanarwar ta kara da cewa wani daga cikin wadanda ake zargi mai suna Shamsudeen Hassan ne ya harbe mai gadin gidan, Barnabas Danlami, yayin da sauran suka gudanar da fashin. Rundunar ta tabbatar da cewa bincike yana ci gaba, tare da alƙawarin gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala.
