Featured
Gwamnan Katsina Ya Musanta Batun Yin Sulhu da Ƴan Ta’adda
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya bayyana a fili cewa gwamnatinsa ba ta taɓa shiga tattaunawa da ‘yan bindiga ba, yana mai jaddada cewa manufarsa ita ce samar da zaman lafiya na gaskiya da dorewa. Ya bayyana haka ne yayin bikin yaye jami’ai 100 na sabon ajin rundunar Community Watch Corps (C-Watch), waɗanda za su fara aiki a ƙananan hukumomi 20 na jihar. Wannan ya biyo bayan jita-jitar cewa gwamnatin Katsina ta shiga tattaunawa da ‘yan ta’adda — wanda gwamnan ya musanta.
Radda ya ce tsarin “Katsina Model” ya dogara ne da al’umma kai tsaye, inda mazauna yankunan da matsalar tsaro ta shafa ke fara tattaunawa da ‘yan ta’addan da suka tuba, yayin da gwamnati ke ba da goyon baya da tabbatar da doka da oda. Ya bayyana cewa wannan tsarin ya samar da zaman lafiya na tsawon watanni a yankuna kamar Jibia, Batsari, Danmusa, Safana, Faskari da Sabuwa.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa da hukumomin tsaro na tarayya kamar Sojojin Sama da Na Kasa da ‘Yan Sanda, inda ya ce hakan ya inganta musayar bayanan sirri da gaggawar daukar mataki. Ya gargadi masu tunanin komawa aikata laifuka cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Nasir Mu’azu, da Shugaban Kwamitin C-Watch, Manjo Janar Junaidu Bindawa (rtd), sun yabawa shirin, suna mai cewa jami’an sun sami horo na musamman kan dabarun yaki, mu’amala da al’umma, da tattara bayanan sirri. Sun kuma bukaci a kara karfafa tsarin jagoranci daga matakin ƙasa zuwa jihar don inganta aiki da gaskiya.
