Connect with us

Featured

Najeriya Za Ta Yi Haɗin- gwiwa Da Ƙasar Sin Domin Ƙarfafawa Mata Manoma

Ma’aikatar kula da harkokin mata da zaman takewa ta Nijeriya, ta gudanar da wani taro irinsa na farko, domin jan hankalin ‘yan kasuwar kasar Sin su zuba jari a bangaren kayayyakin more rayuwa da mata da za su iya cin gajiya.

Yayin taron wanda ya gudana jiya Juma’a a birnin Beijing na kasar Sin, ministar ma’aikatar Imaan Suleiman Ibrahim, ta ce burin shirye-shiryen raya harkokin mata na ma’aikatar, wadanda ke karkashin shirin Sabon Fata na shugaban kasa Bola Tinubu, shi ne karfafa gwiwar mata miliyan 10 da su ingiza burin kasar na bunkasa tattalin arzikinta.

Ta ce makasudin taron shi ne, neman jari ga shirye shiryen ma’aikatar musammam na samar da makamashi mai tsafta ga mata da ake wa lakabi da WINGS da kuma shirin bunkasa karfin mata manoma na WAVE.

Ta ce manufar shirin WINGS bai tsaya kadai ga samar wa mata makamashi mai tsafta na amfanin yau da kullum ba, har da tabbatar da cewa sun shiga ana damawa da su a bangaren samar da makamashin da kuma jagorantar kasar wajen komawa ga amfani da makamashi mai tsafta.

A cewarta, mata ne suka mamaye kaso 70 na manoma da masu kiwon dabbobin gida, amma kuma saboda karancin jari a bangaren, sun kasance koma baya, don haka shirin WAVE ke da zummar karfafa musu gwiwa domin bunkasar karfinsu, ta yadda za su samu karin kudin shiga da dogaro da kansu.

Bugu da kari, minista Imaan Suleiman Ibrahim ta jaddada cewa, an fasalta shirye shiryen ma’aikatar na kyautata harkokin mata, ta yadda za su bude wata sabuwar kafa ta karfafa tattalin arzikin mata da samar musu da jari tare da ba su damar shiga ana damawa da su a harkokin shugabanci ta yadda za gaggauta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, da karfafa tsarin samar da kayayyaki.

Taron ya samu halartar manyan jami’an Sin da Nigeria, ciki har da shugabar kwamitin kula da harkokin mata ta majalisar wakilan Nijeriya Kafilat Ogbara, da masu zuba jari na kasar Sin.

 

 

 

 

 

 

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet