Featured
Donald Trump Ya Hana Zelensky Makamin Tomahawk
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya kasa samun makamin yaki mai linzami na Tomahawk daga Amurka bayan ganawarsa da Shugaba Donald Trump a Fadar White House. Zelensky ya je Washington da fatan samun wannan makami domin amfani da shi wajen kai hare-hare kan Rasha, amma tattaunawar ta karkata zuwa batun neman mafita ga rikicin maimakon bayar da makamai.
Trump ya bayyana cewa bai yi watsi da bukatar Zelensky ba, sai dai manufarsa ita ce kawo ƙarshen rikicin ta hanyar yarjejeniya, ba ta hanyar ƙara zafafa yaki ba. Bayan ganawar, ya bukaci bangarorin biyu — Rasha da Ukraine — da su dakatar da kashe-kashe tare da komawa teburin tattaunawa.
Rahotanni sun nuna cewa wannan matsaya ta Trump ta fito fili tun bayan tattaunawar wayar tarho da ya yi da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, tsawon sa’a biyu da rabi kwanaki biyu da suka gabata. A lokacin, shugabannin biyu sun amince da yin ganawa ta kai tsaye a birnin Budapest domin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin.
Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa Trump ya fi mayar da hankali kan sulhu da sassauta rikicin, maimakon bayar da ƙarin makamai, abin da ke nuna sauyi a matsayar Amurka kan yakin Ukraine-Rasha idan aka kwatanta da tsohuwar gwamnati.
