Connect with us

Featured

Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 3,433 Cikin Watanni 9 — FRSC

Hukumar Kiyaye Lafiyar Hanya ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa mutane 3,433 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 22,162 suka jikkata a hatsarori 6,858 da aka samu daga watan Janairu zuwa Satumba 2025. Shugaban hukumar, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja domin kaddamar da kamfen din “Ember Months” na wannan shekara, wanda ke da nufin rage yawan haɗurra musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.

Mohammed ya ce manyan dalilan haddasa haɗurra sun haɗa da gajiya ko rashin hutu ga direbobi, ɗora kaya fiye da ƙima, ɗaukar fasinjoji a manyan motoci masu kaya, da kuma safarar mai cikin kwalabe na roba. Ya kuma nuna cewa a lokacin “Operation Zero” da aka gudanar daga 15 ga Disamba 2024 zuwa 15 ga Janairu 2025, mutane 432 ne suka mutu, yayin da 2,070 suka jikkata a haɗurra 533. Ya ce kamfen ɗin bana zai mai da hankali kan wayar da kai da ilimantarwa don inganta tuƙi a hanya.

Shugaban FRSC ya bayyana cewa laifukan da ke yawan haddasa haɗurra sun haɗa da gudu fiye da kima, tuƙi cikin maye, karya dokokin hanya, rashin amfani da bel, da kuma amfani da waya yayin tuƙi. Don haka, hukumar za ta tura jami’anta zuwa manyan tituna da wuraren da ake yawan samun haɗurra a fadin ƙasar. Haka kuma, an ƙaddamar da sabon tsarin biometric don samun lasisin tuƙi cikin sauri ba tare da jinkiri ko amfani da takardar wucin gadi ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet