Featured
EFCC Ta Ƙwato Naira Biliyan 500 Cikin Shekara Biyu
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yabawa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) bisa nasarorin da ta samu a yaƙin da take da cin hanci, inda ya ce ta karɓo kadarori da kuɗaɗe da suka haura naira biliyan 500 tare da gurfanar da mutane sama da 7,000 cikin shekara biyu na mulkinsa. Tinubu, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta a wajen taron bita na masu shari’a a Abuja, ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafawa hukumomin yaƙi da rashawa domin tabbatar da gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin shari’a.
A cewar Tinubu, kudaden da EFCC ta karɓo daga hannun masu laifi an sake juyar da su don tallafawa shirye-shiryen jin ƙai kamar lamunin ɗalibai da tsarin bayar da bashi ga masu amfani da kayayyaki. Ya yi kira ga sauran rassan gwamnati da su haɗa kai da kotuna wajen tabbatar da gaskiya da daidaito a fagen shari’a, yana mai cewa, “Ba za mu iya magance cin hanci ba sai mun zama abin koyi.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi gargadi kan jinkirin da ake samu a shari’o’in manyan mutane, yana mai cewa wannan matsala tana sanya shakku a zukatan jama’a. Ya bayyana cewa akwai shari’o’in da suka kai shekara 15 zuwa 20 suna juyawa a kotu saboda dabarun da wasu masu hannu da shuni ke amfani da su wajen tsawaita shari’a, ciki har da fakewa da rashin lafiya da kuma aikace-aikacen da ke jinkirta shari’a.
Olukoyede ya kuma soki wasu alkalai da lauyoyi da ke amfani da fasahohi don kare masu laifi, yana mai cewa hakan na raunana yaƙin da ake yi da cin hanci. Ya ce wasu alkalai na kotunan jihohi na bayar da umarnin da ba ya cikin huruminsu don hana binciken EFCC, lamarin da ke kawo cikas ga aikin hukumar. Ya roƙi kotuna da su kasance masu lura wajen yanke hukunci, musamman a shari’o’in da ke da tasiri ga nasarar yaƙin da ake yi da rashawa a Najeriya.
