Connect with us

Featured

Gwamna Bago Ya Bayar Da Naira Miliyan 42 Ga Iyalan Waɗanda Su Ka Mutu Yayin Fashewar Tankar Mai

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da tallafin naira miliyan ɗaya (₦1m) ga kowane iyalin wanda ya rasu, da kuma naira dubu ɗari biyar (₦500,000) ga kowanne daga cikin waɗanda suka ji rauni a mummunan hatsarin fashewar tanka da ya auku a garin Essa, karamar hukumar Katcha. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa al’ummar yankin a ranar Alhamis 23 ga Oktoba.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 3:45 na rana, lokacin da wata tanka mai ɗauke da fetur ta kife a kan hanyar Bida–Badegi–Agaie. Hukumar Niger State Emergency Management Authority (NSEMA) ta tabbatar da cewa mutane 42 ne suka mutu, yayin da 52 suka jikkata.

Gwamna Bago ya nuna bakin cikinsa kan wannan bala’i, inda ya yi addu’ar samun waraka ga waɗanda ke jinya a asibitin Bida da Abuja. Ya kuma soki halayyar jama’a na zuwa ɗibar da fetur daga tankokin da suka kife, yana mai cewa wannan aiki “laifi ne kuma haɗari ne da ya kamata a daina shi gaba ɗaya.”

A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar, Bago ya bayyana cewa fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Aliko Dangote ya yi alƙawarin gyara hanyar Mokwa–Lambata, sannan gwamnati za ta gina sabuwar cibiyar kiwon lafiya ta farko a Essa domin tallafa wa al’ummar yankin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet