Connect with us

Featured

Jami’ar ABU Ta Musanta Batun Yunƙurin Ƙirƙirar Makamin Nukiliya

Jami’ar Ahmadu Bello University (ABU), Zaria, ta karyata wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na cikin wani shirin sirri na ƙirƙirar makamin nukiliya ga Najeriya. Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar a Zariya.

A cewarsa, bidiyon da aka samar ta hanyar fasahar AI ƙarya ne kuma an yi shi ne domin yaudara da yaɗa bayanan da ba su da tushe game da shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da Najeriya ke gudanarwa. Umar ya ce zargin cewa masana na ABU sun taba haɗin gwiwa da AQ Khan network daga Pakistan ko kuma sun taɓa samun kayan aikin nukiliya tun a shekarun 1980 ba gaskiya ba ne.

Ya bayyana cewa a lokacin da ake magana a kai, yawancin masana da ke Cibiyar Binciken Makamashin Nukiliya ta ABU (CERT) har yanzu suna karatu a ƙasashen waje, don haka ba su da wata alaƙa da shirye-shiryen ɓoye na ƙera makamin nukiliya. Umar ya ƙara da cewa a shekarar 1987, kayan aikin nukiliya na ABU bai wuce na’urar Neutron Generator ba, wadda ta fara aiki a 1988.

Jami’ar ta nanata cewa dukkan harkokin makamashin nukiliya a Najeriya ana gudanar da su ne bisa tsarin kasa da kasa ta IAEA, don amfanin zaman lafiya da ci gaban ƙasa. ABU ta kuma jaddada aniyarta na ci gaba da amfani da kimiyyar nukiliya wajen cigaban ilimi da tattalin arziki, ba wai wajen gina makaman yaƙi ba.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet