Featured
Likitoci Za Su Tsunduma Yajin Aiki Ranar 1 ga Nuwamba
Kungiyar Likitocin Gwamnati masu koyon aiki a asibitocin gwamnati (NARD) ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin daga ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025, bayan karewar wa’adin kwanaki 30 da ta bai wa Gwamnatin Tarayya don cika wasu muhimman bukatu. Shugaban kungiyar, Dr. Muhammad Suleiman, ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai, inda ya ce Majalisar Zartarwar Kungiyar ta yanke wannan matsaya ne bayan tattaunawa ta gaggawa da aka yi ta yanar gizo.
Dr. Suleiman ya bayyana cewa kungiyar ta gaji da yadda gwamnati ke jinkirta aiwatar da alkawuran da ta ɗauka, ciki har da biyan ragowar ƙarin albashi na 25% da 35% karkashin tsarin CONMESS, da kuma biyan kudaden kayan aiki na shekarar 2024 da ba a cika ba. Haka kuma kungiyar ta koka kan kora likitoci biyar daga Asibitin Koyarwa na Lokoja, tana mai cewa hakan ba daidai ba ne, musamman a lokacin da ƙasar ke fama da yawan barin ƙasa da likitoci ke yi.
A cikin korafe-korafenta, NARD ta kuma nuna rashin jin daɗi kan matsalolin karin girma da biyan bashin albashi da suka jima a asibitocin tarayya, da ware likitocin masu koyon aiki daga tsarin albashin ma’aikatan gwamnati, wanda ke haifar musu da rashin amincewa da matsayinsu na ƙwararru. Haka kuma, ta soki yadda aka saukar da matsayi da albashi ga sabbin likitocin koyon aiki daga CONMESS 3 Step 3 zuwa CONMESS 2 Step 2, abin da ke jawo rashin daidaito da ƙarancin albashi.
Kungiyar ta ce ba za ta janye wannan mataki ba har sai an biya bukatunta 19 gaba ɗaya, tana gargadin cewa idan gwamnati ta kasa daukar mataki cikin gaggawa, yajin aikin da za ta fara zai durƙusar da harkokin lafiya a asibitocin gwamnati, inda likitocin koyon aiki ke da muhimmiyar rawa wajen kula da marasa lafiya.
