Featured
PDP Ta Hana Sule Lamido Fom Ɗin Tsayawa Takarar shugabancin jam’iyyar
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya nuna takaicinsa bayan ya kasa samun fom ɗin takarar Shugabancin jam’iyyar PDP a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya yi barazanar kai jam’iyyar ƙara a kotu. Lamido, wanda ya isa Wadata Plaza da safiyar ranar Litinin 27 ga Oktoba, tare da magoya bayansa domin sayen fom ɗin, ya bayyana cewa yana da cikakken niyyar tsayawa takara a babban taron zaben shugabannin jam’iyyar da za a gudanar a Ibadan ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.
A cewar tsohon Ministan Harkokin Waje, abin da ya faru rashin adalci ne da ke nuna an kulle ƙofar takara ga wasu ‘yan jam’iyyar. Ya ce ba zai lamunci a hana shi fadin albarkacin bakinsa ba, yana mai cewa zai bi ta kotu idan ba a ba shi damar sayen fom ɗin ba.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnoni na PDP sun riga sun amince da tsohon Ministan Harkokin Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin ɗan takarar su, abin da ke nuna yiwuwar an cimma matsayar “yarjejeniyar haɗin kai” don hana Lamido da wasu tsoffin gwamnonin — irin su Ibrahim Shekarau da Ahmed Makarfi — tsayawa takara.
Lamido, wanda ya tabbatar da niyyarsa ta neman kujerar a shafinsa na Facebook kafin zuwa hedkwatar jam’iyyar, ya ce “da ikon Allah, yau zan je Wadata Plaza domin sayen fom ɗin takarar Shugaban Jam’iyyar PDP,” yana mai jaddada cewa zai tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙinsa a cikin jam’iyyar.
