Featured
Tattalin Arzikin Najeriya Ya Fara Bunƙasa – Wale Edun
Ministan Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arzikin Najeriya, Mista Wale Edun, ya tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar ya fara dawowa hayyacinsa bayan wahalhalun da aka fuskanta a shekaru biyu da suka wuce. A cewar Edun, Najeriya ta “kalli baya” ta kuma shiga sabon babi na bunƙasa tattalin arziki, inda ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shawo kan manyan matsalolin da suka haɗa da hauhawar farashi, ƙarancin jarin waje, da rusasshen tsarin musayar kudi. Ya ce a halin yanzu, GDP ta ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari, yayin da hauhawar farashi ta sauka zuwa kashi 18.02 cikin ɗari, sannan kudin waje ya daidaita, inda bambanci tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage ya ragu sosai.
Edun ya ce bayan cire tallafin man fetur da haɗa tsarin musayar kuɗi a 2023, gwamnatin ta tsabtace kasuwa daga almundahana, duk da cewa hakan ya janyo tashin farashin man fetur daga kusan N238 zuwa kusan N950 a yanzu. Duk da haka, ya bayyana cewa dabarun gwamnati suna rage tasirin matsin lamba ga ‘yan ƙasa, musamman ta hanyar tallafin kuɗi kai tsaye ga gidaje sama da miliyan takwas da ɗigo ɗaya (8.1m), tare da shirin ƙara kai tallafin ga gidaje miliyan 15 gaba ɗaya.
A fannin abinci kuwa, ministan ya ce farashin kayan masarufi na sauka a hankali, inda ya bayar da misali da buhun shinkafa da a bara yake kusan N120,000 amma yanzu yana zagaye N80,000. Ya ce gwamnati tana aiki don tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya ci gaba da sauka, tare da bai wa manoma ƙarin tallafi domin su koma gona a lokacin dasa shuka mai zuwa.
Dangane da bashi kuma, Edun ya bayyana cewa duk da ci gaban da aka samu, har yanzu bashin ƙasar yana da nauyi, amma sabuwar dokar haraji da aka sanya hannu a kai a watan Yuni 2025 za ta taimaka wajen faɗaɗa hanyoyin samun kudaden shiga da rage maguɗin haraji. Ya ce gwamnatin Tinubu na amfani da haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu don bunƙasa ayyukan tattalin arziki kamar aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano da kuma shimfiɗar igiyar intanet mai tsawon kilomita 90,000. Edun ya ƙara da cewa gwamnati na fatan samun ci gaban tattalin arziki da zai kai kashi 7 cikin ɗari nan da shekarar 2028, idan aka ci gaba da daidaiton manufofi da haɗin kan al’umma.
