Connect with us

Featured

Hatsarin Kwalekwale Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mahaifiya Da Ƴarta a Borno

Wani mummunan hatsarin jirgin ruwa ya faru a karamar hukumar Hawul ta jihar Borno, ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata mai shekara 35 mai suna Habiba Abubakar da ’yarta Adama mai shekara tara, sakamakon kifewar jirgin da suke ciki yayin dawowa daga gona. Rahoton PUNCH Metro ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Asabar, 26 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, lokacin da suka shiga kogin da ke kusa da garin Ghung domin komawa gida.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce ƙarfi da gudun ruwan kogin ne ya jawo jirgin ya kife. A cewarsa, jami’an tsaro tare da masu aikin ceto na yankin sun gano gawarwakin mamatan daga kogin bayan wani lokaci, kuma babu alamun tashin hankali ko rauni a jikinsu.

An dauki hotunan gawarwakin domin bincike kafin a kai su Asibitin Garkida da ke karamar hukumar Gombi a jihar Adamawa, kasancewar shi ne asibiti mafi kusa. Wani kwararren tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana a shafinsa na X cewa likitan da ya duba su a asibiti ya tabbatar da cewa sun mutu tun kafin isarsu.

Jami’an Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) na jihar Borno sun kaddamar da bincike kan dalilan hatsarin, yayin da aka mika gawarwakin ga iyalansu domin jana’iza bisa tsarin Musulunci. Wannan lamari ya kara yawan lokutan kifewar jirgin ruwa da ake ta fuskanta a yankin Arewa maso Gabas na ƙasar a ’yan watannin nan.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet