Connect with us

Featured

Kotu Ta Dakatar Da Babban Taron PDP Na Ƙasa

Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da gangamin taronta na ƙasa da aka shirya yi a Ibadan, jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba 2025, bisa zargin take dokokin zaɓe da na cikin gida na jam’iyyar. Alƙali James Omotosho ne ya yanke hukuncin, yana cewa PDP ta gaza bin ka’idojin kundinta, kundin tsarin mulkin ƙasa, da kuma dokokin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Wadanda suka shigar da ƙarar su ne wasu shugabannin jam’iyyar daga jihohin Imo, Abia, da Kudu maso Kudu, inda suka yi zargin cewa taron da ake shirin gudanarwa zai sabawa dokokin jam’iyyar da na ƙasa. Sun nemi kotu ta hana PDP ci gaba da shirye-shiryen taron har sai ta gyara kura-kuran da ake gani a cikin tsarin zaben shugabanni.

Alƙali Omotosho ya bayyana cewa PDP ta kasa gudanar da sahihan tarukan jihohi kafin shirya taron ƙasa, wanda hakan ya saba wa doka. Ya umurci jam’iyyar da ta “koma ta shirya ta gyara gida,” sannan ta ba INEC sanarwar kwanaki 21 kafin sake shirya sabon taro. Haka kuma ya haramta wa INEC karɓar ko amincewa da sakamakon wani taron PDP da bai bi ƙa’ida ba.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙalubalen da PDP ta gabatar cewa al’amarin lamari ne na cikin gida, inda ta tabbatar cewa idan jam’iyya ta karya dokokin da kundin tsarin mulki da Electoral Act suka tanada, to kotu na da hurumin shiga tsakani. Wannan hukunci ya jefa jam’iyyar PDP cikin rikicin cikin gida a daidai lokacin da ake shirin sabon zaɓen shugabanni na ƙasa.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet