Connect with us

Featured

Jam’iyyun Adawa Sun Zargi Tinubu Da Tilastawa Ƴan Siyasa Sauya Sheƙa Zuwa APC

Wasu manyan jam’iyyun adawa a Najeriya sun zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da kudaden gwamnati da hukumomin yaki da cin hanci wajen matsa wa ‘ya’yansu su koma jam’iyyar APC. Jam’iyyun PDP, NNPP, da CUPP sun bayyana cewa APC ta shiga wani hali na rikici, duk da cewa ana ta samun fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa suna sauya sheka zuwa gare ta. Sun ce wannan lamari yana nuna yunƙurin kafa jam’iyya ɗaya tilo a ƙasar, abin da zai iya zama barazana ga dimokuraɗiyya.

Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya ce APC na amfani da karfin gwamnati wajen jan hankalin mambobin jam’iyyunsu, amma ya yi hasashen cewa jam’iyyar za ta ruguje nan gaba. A cewarsa, PDP ita ce kadai jam’iyyar da ke da ingantaccen tsari daga matakin ƙasa har zuwa ƙananan hukumomi, kuma ‘yan Najeriya za su gane gaskiya su dawo gare ta kafin zaben 2027.

Shi ma kakakin NNPP, Oladipo Johnson, ya bayyana damuwa cewa yawan sauya sheka zuwa APC na iya lalata tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar. Ya ce irin wannan abu ya taba faruwa da PDP a da lokacin da take mulki, inda daga bisani jam’iyyar ta watse saboda rashin daidaito. Ya yi gargadin cewa tursasawa ko son kai a siyasa ba zai taba haifar da ci gaba ba, domin babu wata jam’iyya da za ta iya zama tilo a Najeriya.

A nasa bangaren, kakakin CUPP, Mark Adebayo, ya ce wannan tsarin sauya sheka ba hatsari ba ne, amma wata dabara ce da gwamnatin Tinubu ke amfani da ita don kafa mulkin jam’iyya ɗaya. Ya ce hakan abin kunya ne ga demokuraɗiyyar Najeriya, yana kuma gargadin cewa idan APC ta rasa mulki, za ta tarwatse saboda yawancin ‘yan siyasa a ƙasar ba sa da ra’ayi ko akida ta gaskiya sai dai neman karfi da iko. Sai dai APC ta musanta wannan zargi, inda kakakinta Bala Ibrahim ya ce duk masu shiga jam’iyyar suna yin hakan ne da son ransu saboda nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet