Featured
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Abuja Ya Kori Ma’aikata 800
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja, wato AEDC, ya tabbatar da fara aiwatar da wani babban tsarin sake fasalin harkokinsa domin inganta yadda ake samar da wutar lantarki ga al’umma da kuma inganta ayyukan ma’aikata.
A bisa wannan sauyi, kamfanin ya tabbatar da cewa ya dauki matakin daga ciki wanda ya hada da karin girma ga ma’aikatan da suka nuna kwarewa, sallamar wadanda suka kai lokacin ritaya, da kuma korar wadanda ba su kai matsayin da ake bukata ba. Wannan ya biyo bayan wani tsarin ci gaba da horar da ma’aikata da kuma karfafa sashen kula da kwastomomi don tabbatar da hidima mai inganci.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa akalla ma’aikata 800 ne abin ya shafa, duk da cewa tun farko an yi niyyar sallamar ma’aikata 1,800 kafin kungiyoyin kwadago su shiga tattaunawa da kamfanin. Ana ganin wannan yunkuri a matsayin wani bangare na kokarin rage yawan kashe kudi da inganta yawan aiki a lokacin da ake kara matsa lamba ga kamfanonin wutar lantarki su kara inganci da tabbatar da wuta mai dorewa.
AEDC ta ce wannan mataki ba wai kawai rage ma’aikata ba ne, sai dai wani yunkuri na gina kamfani mai tsari, inganci da kulawa da bukatun jama’a. Ta ce za ta ci gaba da zuba jari a cikin sabbin kayayyakin lantarki, fasahohi na zamani, da kuma hanyoyin gudanarwa na zamani domin kara inganta samar da wuta a Abuja, Kogi, Nasarawa da Niger.
