Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kawo Ƙarshen Matsalar Ƙarancin Abinci a Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabbin tsare-tsare na bunkasa harkar noma domin dakile ƙarancin abinci, ƙara yawan amfanin gona da rage asarar amfanin gona da ake yi bayan girbi da ake kiyasta ya kai sama da dala biliyan 10 duk shekara. Ministan Noma da Tsaro na Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin Najeriya, don haka an fara aiwatar da sauye-sauye domin tabbatar da wadataccen abinci da ingantaccen tsarin ajiya.
A cewar Ministan, gwamnati na ƙara kuzarin amfani da injinan noma, faɗaɗa ban-ruwa da kuma karfafa samar da cibiyoyin ajiya a matakai daban-daban na ƙasar. Haka kuma an kafa shirin Nigeria Postharvest Systems Transformation Program (NiPHaST) don rage asarar amfanin gona bayan girbi da kuma tabbatar da daidaiton farashin abinci a kasuwanni. Har ila yau, an fara sabbin dabarun noman alkama a yankunan da ake dogaro da ruwan sama kamar Filato, Taraba da Cross River.
Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙara kuɗi ga Bankin Noma da ya kai naira tiriliyan 1.5, tare da kafa tsarin bai wa ƙananan manoma rance na naira biliyan 250. Haka nan an kaddamar da shirin injinan noma ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanin Heifer Nigeria, domin bai wa manoma damar amfani da taraktoci da sauran injina cikin sauƙi da ragin kuɗi.
A gefe guda, an bayyana cewa ana mayar da hankali wajen samar da kayan aikin ban-ruwa, gina hanyoyin shiga gonaki, rijiyoyin hasken rana, da bunkasa kasuwanni a yankunan karkara. Gwamnatin ta ce duk waɗannan matakai na shiga ne cikin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Tinubu domin tabbatar da cin gashin kai a fannin abinci da dawo da martabar Najeriya a matsayin jagora a samar da abinci a Afirka ta Yamma.
