Connect with us

Addini

Hajj 2026 : Shirye-shiryen Tunkarar Aikin Hajjin 2026 Ya Yi Nisa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta kammala binciken otel da cibiyoyin girke-girke a birnin Madina a kokarinta na tabbatar da ingantattun shirye-shirye tun da wuri don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026. An gudanar da wannan duba ne daga 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba, karkashin jagorancin Kwamishinan Tsare-tsare da Bincike, Farfesa Abubakar Yagawal, tare da hadin gwiwar wakilai daga Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, mambobin hukumar, da hukumar jin dadin alhazai ta jihohi.

A lokacin ziyarar, tawagar ta tantance fiye da otel 20 a yankin Markaziyya na Madina da kuma cibiyoyin girke abincin alhazai guda bakwai. Hakan ya hada da duba takardun aiki, tsaro, tsabtar muhalli, da bin ka’idojin Saudiyya da na NAHCON kan masauki da abinci. Sakamakon farko ya nuna cewa yawancin masu bada sabis sun inganta hanyoyin tsaro da tsaftace muhalli.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya yi gargadin cewa aikin tabbatar da jin dadin alhazai yana bukatar gaskiya, kwararru, da rashin nuna son zuciya. Ya ce hukumar ba za ta lamunci sabis mara inganci ba, domin lafiyar alhazai da walwalarsu sune babban abin da ake muradi. Ya kara da cewa dukkanin rahoton ziyarar za a gabatar da shi don daukar matakin da ya dace kafin bude sabbin kwangiloli.

A cikin jadawalin shirye-shiryen Hajjin 2026, NAHCON ta jaddada cewa jihohi da kamfanonin aikin hajji dole su bi lokutan da aka tsayar, ciki har da biyan kuɗi kafin 1 ga Oktoba 2025 da kammala kwangiloli kafin 4 ga Janairu 2026. Haka kuma, hukumar ta nanata cewa ranar karshe ta fitar da visa ita ce 20 ga Maris 2026, wanda ba za a yarda a karya wannan lokaci ba domin kaucewa tangarda ga tafiyar alhazai.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet