Connect with us

Featured

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Jami’an DSS 115 Da Aka Kora Daga Aiki

Gwamnatin Tarayya ta sallami jami’an Hukumar Tsaro ta SSS (DSS) guda 115 bayan an gano laifuffuka daban-daban da ake zargin su da aikatawa, ciki har da almundahana, karya doka, da kuma yin amfani da takardun bogi. Majiyoyi daga cikin hukumar sun bayyana cewa akwai wasu daga cikin jami’an da suka rika fallasa bayanan sirri na aikin, abin da ya zama barazana ga sahihancin hukumar.

Wadanda abin ya shafa sun hada da masu matsalolin ladabtarwa tun a zamanin tsohon Darakta-Janar na DSS, amma wasu daga cikinsu sun sake maimaita laifin ne bayan sabon Darakta-Janar, Adeola Ajayi, ya hau mulki. Sabon shugabancin dai ya dukufa wajen tsaftace hukumar domin dawo da martaba, tsari, da kuma tabbatar da gaskiya a cikin aikin leken asiri.

Bugu da ƙari, wasu daga cikin jami’an sun yi ƙaura zuwa kasashen waje ba tare da izini ba, wanda ya keta ka’idojin aiki. Akwai kuma wadanda suka gabatar da takardar karatu daga makarantun kasashen waje da suka yi karatu na dan lokaci, ko kuma takardun addini da ake kokarin gabatarwa a matsayin digiri. Hukumar ta fitar da hotuna da bayanansu domin gargadin jama’a kada su ci gaba da mu’amala da su a matsayin jami’an DSS.

Sai dai wani masanin tsaro, Kabir Adamu, ya soki matakin bayyana hotunan jami’an da aka kora, yana mai cewa hakan na iya jawo barazana ga rayukansu, tare da yiwuwar kungiyoyin ta’addanci su nemi amfani da su ko su rama abin da ya gabata. Duk da haka tsohon Darakta na DSS, Mike Ejiofor, ya ce wannan matakin na daga cikin tsare-tsaren gyaran harkokin hukumar a halin yanzu.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet