Featured
Ɓarawo Ya Kutsa Gidan Gwamnatin Jihar Kano Ya Sace Mota Ƙirar Hilux
Wasu rahotanni daga Kano sun bayyana cewa wani barawo ya kutsa cikin Fadar Gwamnatin Jihar Kano da safiyar Litinin, inda ya sace wata mota kirar Toyota Hilux da ke cikin jerin motocin mataimakin gwamna. Lamarin ya faru ba tare da jami’an tsaro sun lura da shi ba, lamarin da ya tayar da hankalin ma’aikata da jami’an tsaro na fadar gwamnati.
Majiyoyi daga cikin Fadar sun ce bayan an duba bidiyon CCTV, an gano cewa barawon ya shiga ta ƙofa mai lamba 4, sannan ya fita daga babban ƙofar gidan gwamnati cikin natsuwa. Hakan ya nuna akwai gibin tsaro mai girma musamman saboda ofishin mataimakin gwamnan ba ya samun kulawar jami’an tsaro sai a lokutan aiki.
Direban motar da aka sace, wanda aka bayyana da suna Shafiu Sharp-Sharp, an tsare shi na ɗan lokaci domin bincike. Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun fara bincike, yayin da Babban Jami’in Tsaron Gwamnatin Kano (CSO) ke sake nazarin faifan bidiyon domin gano wanda ya aikata laifin.
Hukumar tsaro ta riga ta baza hoton motar da bayananta ga sassan tsaro na ƙasa baki ɗaya, domin tabbatar da an kama wanda ya aikata wannan abin kunya, wanda ke nuna gagarumar matsalar tsaro a cikin Fadar Gwamnatin Jihar KƁarawo Ya Kutsa Gidan Gwamnatin Jihar Kano Ya Sace Mota Ƙirar Hiluxano.
