Featured
Rikicin Cikin Gida Ne Yasa Na Fice Daga Jam’iyyar NNPP – Engr. Sagir Ƙoƙi
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Hon. Sagir I. Koki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a cikin wata takarda da ya aikawa shugaban gundumar Zaitawa a ranar 11 ga Nuwamba, 2025.
A cikin wasikar, Koki ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bisa hakkin da kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara) da kuma kundin tsarin NNPP suka ba shi. Ya ce rikicin cikin gida da ya dabaibaye shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa ya jefa shi cikin hali na rashin iya ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ga al’ummar Kano Municipal.
Ya bayyana cewa, wannan matsalar ta sa ya kasa wakiltar jama’arsa yadda ya kamata a majalisar wakilai, saboda haka ya ga dacewar ya ja gefe domin baiwa kansa damar ci gaba da hidimar jama’a ta wata hanya daban.
Hon. Sagir Koki ya gode wa jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi ya yi aiki a karkashinta, yana mai jaddada cewa ya samu gogewa da haɗin kai daga shugabanni da mambobi a matakai daban-daban, tare da yi musu fatan alheri a cigaban da ke tafe.
