Featured
NDC ta yi babban kuskure wajen zaɓar Kwankwaso a matsayin mataimakin Peter Obi – NNPP
Jam’iyyar NNPP ta ce, jam’iyyar NDC ta yi babban kuskure wajen zaɓar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi a zaɓen 2027.
Sakataren NNPP na ƙasa, Ogini Olaposi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya soki matakin da NDC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, suka ɗauka.
Read Also : Iyalan El-Rufai sun ba wa Christopher Musa kwanaki bakwai ya janye kalamansa ko su garzaya kotu
Olaposi ya ce a ra’ayinsu, zaɓar Kwankwaso a matsayin abokin takarar Obi na iya jefa jam’iyyar NDC cikin matsala, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
