Connect with us

Featured

Iyalan El-Rufai sun ba wa Christopher Musa kwanaki bakwai ya janye kalamansa ko su garzaya kotu

Iyalan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa mai ritaya, wa’adin kwanaki bakwai ya janye zarge-zargen da ya yi wa tsohon gwamnan, ko kuma su ɗauki matakin shari’a a kansa.

A wata sanarwa da ɗan El-Rufai Bello El-Rufai, ya fitar a Litinin din nan a madadin iyalan, ya ce Janar Musa ya yi zargin ne yayin wata hira kai tsaye, a shirin “Politics Today” na Channels Television ranar 3 ga Satumba. Ministan ya zargi El-Rufai da shirya kashe mutane a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

Read Also : Tinubu ba shi da ƙwarewar da zai iya magance matsalar tsaron Najeriya – APM

Iyalan sun ce ministan bai gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin ba, don haka suka buƙaci ya gabatar da hujjojin, ko kuma ya janye kalaman tare da ba da haƙuri a bainar jama’a. Lauyoyin El-Rufai sun kuma buƙaci ministan ya bayyana dukkan hujjoji, rahotanni da bayanan da ya dogara da su wajen yin zarge-zargen.

Bugu da ƙari, lauyoyin sun buƙaci Janar Musa, ya yi alƙawarin ba zai sake maimaita kalaman ba, tare da neman diyyar naira biliyan 10 kan abin da suka ce illa ce ga martabar El-Rufai. Wasikar ta ce idan ba a samu amsa mai gamsarwa cikin kwanaki bakwai ba, El-Rufai zai maka ministan a kotu, inda zai nemi a ayyana kalaman a matsayin ɓata suna da ƙarya, tare da neman diyya da sauran matakan da doka ta tanada.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet