Featured
NNPP Ta Kori Hashimu Dungurawa
Shugabannin jam’iyyar NNPP na mazaɓar Gargari da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa sun sanar da korar Shugaban Jam’iyyar na jihar Kano, Dr. Hashimu Sulaiman Dungurawa. Sanarwar ta fito ne ta bakin Shugaban mazaɓar, Shu’aibu Hassan, yayin wani taron manema labarai.
Sun ce an ɗauki matakin dakatar da Dungurawan ne bisa zargin tada fitina a jam’iyyar, da kuma korar muhimman ’ya’ya ba bisa ƙa’ida ba. Haka kuma sun zarge shi da zagi da aibata Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, abin da suka ce ba za su lamunta ba.
Kazalika, shugabannin sun ce Dungurawa ya ƙi halartar tarukan masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar tare da yi mata zagon ƙasa. Jam’iyyar ta bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare ƙima da martabarta, a daidai lokacin da NNPP ke fuskantar rikicin cikin gida kan batun sauya sheƙar gwamnan zuwa APC.
