Connect with us

Featured

DSS Ta Gurfanar Da Matashi a Gaban Kotu Bayan Ya Bayyana Burinsa Na Son Ayi Juyin Mulki a Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasa (DSS) ta gurfanar da wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhuma mai alaka da kiran yin juyin mulki a Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa Onukwume ya wallafa saƙonni a shafinsa na X (Twitter) inda yake kira da a kifar da gwamnatin jam’iyyar APC da kuma tallafawa rundunar soji wajen karɓar mulki.

A cewar DSS, waɗannan saƙonni sun saba wa dokokin ƙasa bisa tanadin Sashe na 46A(1) da 59(1) na Criminal Code Act, da kuma Sashe na 24(1)(b) na dokar Cybercrime (Prohibition, Prevention, etc.) Act 2024. An bayyana cewa, a cikin saƙonninsa, Onukwume ya zargi shugaban ƙasa Bola Tinubu da “sayar da ƙasar ga kasashen yamma,” tare da cewa “sojoji ne kaɗai za su iya ceto Najeriya.”

An ce matashin, wanda ke zaune a Oyigbo a jihar Rivers, zai bayyana a gaban kotu a makon nan domin amsa tambayoyi kan tuhume-tuhume guda shida da DSS ta gabatar a kansa. Lamarin na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da musayar ra’ayoyi a fadin ƙasar kan zargin da wasu ke yi cewa akwai makirci na juyin mulki da wasu sojoji ke shiryawa.

Sai dai rundunar soji ta ƙaryata wannan zargi, tana mai cewa ba a sami wata alama ta juyin mulki ba, kuma babu wani jami’in da ake tsare da laifin hakan. Masana da kungiyoyin farar hula sun ja kunnen jama’a kan illar kiran irin wannan abu, suna jaddada cewa ya zama wajibi a kare dimokuraɗiyyar Najeriya daga duk wani yunƙurin kifar da ita.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet