Featured
Rundunar Ƴansanda Ta Kama Ɗalibai 21 Bisa Zargin Shiga Ƙungiyoyin Asiri
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta kama dalibai 21 na makarantar Ogioma Public Secondary School da ake zargi da shiga ƙungiyoyin asiri. An kama su ne bayan da aka hana su kai hari ga Osemwende Public Secondary School, inda suka iso makarantar a babura domin aiwatar da abin da ake zarginsu da shi.
A cewar kakakin rundunar, Moses Yamu, daliban masu shekaru tsakanin 13 zuwa 17 sun iso makarantar da ake shirin kaiwa hari ne a ranar 12 ga Nuwamba bayan sun riga sun yada barazana cewa za su “kaddamar da yaƙi,” su ƙona makaranta, su kuma jikkata dalibai da malamai. Sai dai rundunar Loveworld Division ta hana kai farmakin, inda ta kama 21 daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere.
’Yan sanda sun gano adduna huɗu da sarƙa a wajen wadanda aka kama, kuma an ce malaman makarantun biyu tuni aka gayyace su domin karin bayani. An gurfanar da yaran a kotu, inda takwas daga cikinsu aka tura kurkuku, yayin da 13 aka mika su ga iyayensu tare da sharadin su dawo da su kotu a ranar 28 ga Nuwamba.
Kwamishinan ’Yan Sandan Edo, Monday Agbonika, ya yi kira ga iyaye da makarantu su kula da abokan hulɗar yaransu, su kuma gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani abu da ake zargi. Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ta kafa sabuwar dokar hana ɗabi’ar asiri a Janairu 2025, wadda ta tanadi hukuncin shekaru 21 ga duk mai shiga ko tallafawa irin wannan ƙungiya, tare da tsauraran matakan hukunci domin kare makarantu da al’umma.
