Connect with us

Featured

Gobara Ta Hallaka Miji Da Matarsa Da Ƴaƴansu a Kano

A kalla mutane hudu ne ƴan gida ɗaya suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi da safiyar Laraba a unguwar Kundila Layin Baba Impossible, cikin ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:13 na asuba, ranar Laraba, 19 ga Nuwamba 2025, lokacin da wutar ta mamaye ɗakin da iyalin ke zaune.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari ta bakin mai magana da yawunta, Saminu Abdullahi, wanda ya ce jami’insu Abba Datti ne ya fara bayar da rahoton tashin gobarar. Ya bayyana cewa zuwa lokacin da ma’aikatan suka isa wurin, gobarar ta riga ta cinye ɗakuna biyu, falo, kicin da bandaki, tare da kulle mazauna gida a ciki.

A cewar rahoton da Kakaki24 ta tattara, wadanda suka mutu sun haɗa da mai gidan, Shodandi mai shekara 43; matarsa Rafi’a mai shekara 30; da ‘ya’yansu mata biyu—Mardiya mai shekara uku da Yusira mai shekara ɗaya da rabi. Sai dai an samu ceto yaro ɗan shekara 12, Aminu Shodandi, wanda ma’aikatan kashe gobarar suka yi nasarar fito da shi da ransa.

Hukumar ta bayyana ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, tare da jan hankalin al’umma da su kula da amfani da abubuwan da ka iya jawo wuta musamman a irin wannan lokacin. Bincike na farko ya nuna cewa maganin sauro “mosquito coil” da aka kunna kafin bacci shi ne ya haddasa tashin gobarar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahisholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet