Connect with us

Featured

Bai Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Riƙa Sulhu Da Ƴan Ta’adda Ba – Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bukaci gwamnatin tarayya ta daina bayar da hakuri ko tattaunawa da ‘yan ta’adda, yana mai cewa lokaci ya yi da za a dauki mataki mai tsauri. Ya bayyana hakan ne a Jos, lokacin taron Plateau Unity Christmas Carol da Praise Festival, ranar Juma’a 28 ga Nuwamba, 2025.

Obasanjo ya nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe da sace-sace a Arewa, inda daruruwan mutane suka fada tarkon ‘yan bindiga makonni biyun da suka gabata. Ya ce halin da kasar ke ciki ya nuna gazawar gwamnati, don haka ‘yan Najeriya na da damar neman taimakon kasashen duniya idan gwamnati ta kasa kare su.

A cewarsa, sabuwar fasaha kamar jiragen sama marasa matuki na iya goge ‘yan ta’adda cikin sauki, amma gwamnati ta kasa amfani da damar. Obasanjo ya tambaya dalilin da yasa ake tattaunawa da masu garkuwa da mutane, alhali akwai hanyoyin da za su tarwatsa su cikin sauri. A wannan bangare, Kakaki24 ta lura cewa kalamansa na zuwa ne bayan fargabar da ta yi kamari a Arewa sakamakon hare-hare a Niger, Kebbi, Kwara da Kano.

Ya kara da cewa tun kafin ya bar mulki, gwamnati na da damar gano duk wanda ya aikata laifi a ko’ina cikin Najeriya, kuma yanzu fasahar zamani ta fi inganci. Don haka ya bukaci gwamnati ta tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro, maimakon bada hakuri ko sulhu da wadanda ke kashe ‘yan kasa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet