Featured
Sojoji Sun Ceto Ƴan Mata 12 da Boko Haram Suka Sace a Borno
Borno — Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da ceto ’yan mata 12 da Boko Haram/ISWAP suka yi garkuwa da su a yankin Mussa, ƙaramar hukumar Askira/Uba, jihar Borno. An ce an sace su ne ranar 23 ga Nuwamba yayin da suke aikin girbi a gonakin iyayensu. A sanarwar da rundunar ta wallafa a Facebook, an ce an kai samamen ne bisa sahihan bayanan sirri.
Sojojin Operation Hadin Kai sun ce an kubutar da su ne ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, bayan wani gaggawar farmaki a kudancin Borno. Rundunar ta ce an kwashe waɗanda aka ceto zuwa sansanin tsaro domin a duba lafiyarsu tare da ba su kulawar likitoci da goyon bayan ƙwararrun masu kula da fargaba. A cewar rundunar, al’ummar yankin sun yi murna matuƙa da wannan nasarar.
Kakaki rundunar ya ce bayan kammala binciken likitanci da shawarwari, za a mayar da yaran zuwa ga iyalansu. Rundunar sojin ta yaba wa hadin kan jami’an tsaro da bayanan da al’umma suka bayar, lamarin da ya taimaka wajen nasarar aikin. A Kakaki24 mun tattara cewa sojoji sun ce har yanzu suna ci gaba da binciko sauran ragowar ’yan kungiyar a kudancin Borno.
Sun kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanan sirri don dakile barazanar ta’addanci. Sun lissafa sunayen yaran da aka ceto, wadanda shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 20. Rundunar ta ce za ta ci gaba da sintiri don kare fararen hula da kuma hana sabbin hare-hare a yankin.
