Connect with us

Featured

Ban Yarda Da Biyan Kuɗin Fansa Ko Tattaunawa Da Ƴan Bindiga Ba – Christopher Musa

Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya jaddada cewa ya zama dole gwamnati ta dakatar da duk wani nau’i na tattaunawa da kuma biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga a duk faɗin ƙasar. Ya ce irin waɗannan tattaunawar na ƙara ƙarfin guiwa ga masu aikata ta’addanci.

 

A yayin tantance shi jiya a Majalisar Dattawa, Janar Musa ya bayyana cewa za a ci gaba da fama da rashin tsaro muddin ba a gina ingantaccen rumbun bayanan ’yan ƙasa ba, wanda zai haɗa bayanan tsaro, banki da na tantance mutum wuri guda. Ya ce wannan tsarin shi ne ginshiƙi wajen magance laifuka cikin sauri.

 

Majalisar Wakilai ta yi kira da a gudanar da shari’o’in ta’addanci a bainar jama’a domin rage yawaitar aikata laifukan ta’addanci a ƙasar. Wannan mataki, a cewarsu, zai kara tsoro da kunya ga masu aikata laifi. Kakaki24 ta tattaro cewa ’yan majalisar sun nemi hukumomi su rungumi tsauraran matakai domin kare ƙasa.

 

Yayin jawabi, Janar Musa ya dage cewa duk wata gwamnati da ke son samun nasara kan ta’addanci dole ta nisanci tattaunawa da ’yan bindiga. Ya ce biyan fansa ko shiga sasanci da su ba wai magani ba ne, illa ƙara musu ƙarfi da damar ci gaba da tada hankalin al’umma.

 

 

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet