Connect with us

Featured

Akpabio Ya Buƙaci Natasha Ta Biyashi Naira Biliyan 200 Saboda Cin Zarafinsa

Siyasar Najeriya ta sake daukar sabon salo yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Obot Akpabio, ya shigar da kara, inda ya nemi kotu ta tilasta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bashi diyyar Naira Biliyan 200, bisa zargin ta ɓata masa suna da kuma jingina masa cin zarafin jima’i. A cewar takardun da aka gabatar a Babban Kotun Birnin Tarayya, Akpabio ya ce hirarrakin da Natasha ta yi a talabijin da kafafen intanet sun zubar da mutuncinsa a idon kasa.

Lauyoyinsa sun ce zarge-zargen sun janyo masa “abin kunya, izgili, da mummunar illa ga martabarsa,” musamman ganin yadda kalaman suka bazu a kafofi da dama. Don haka, ya nemi kotu ta tilasta biyan diyyar kuɗi mai yawan gaske, goge dukkan rubuce-rubucen da suka ƙunshi zargin, tare da bayar da uzuri da za a dinga yadawa a talabijin, rediyo da dandalin sada zumunta.

Bayan kasa mika takardar karar kai tsaye ga Natasha, alkalin kotu ya bayar da izinin mika ta ta hannun Sakataren Majalisar Kasa tun ranar 6 ga Nuwamba 2025, wanda ya bai wa kotun damar ci gaba da sauraron shari’ar. A nata bangaren, Sanata Natasha ta tabbatar da samun takardar karar a ranar Juma’a, tana mai cewa ta shirya tsaf domin kare kanta a gaban kotu, bayan an hanata gabatar da korafinta a gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa a baya.

Natasha ta ce lokaci ya yi da za ta bayyana dukkan hujjoji, tana mai jaddada cewa an nemi cin zarafinta, kuma kin amincewarta ne ya haifar da “tsangwama da ramuwar gayya ta siyasa.” Ta aika sako kai tsaye ga Akpabio: “Sai mun hadu a kotu.” Ana sa ran shari’ar za ta janyo cece-kuce mai daukar hankali, ganin yadda za ta dauki nauyin tantance yadda siyasar Najeriya ke tafiyar da kararraki na cin zarafi a matakin manyan mukamai.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet