Featured
Gaskiyar Dalilin Da Yasa Badaru Yayi Murabus Daga Kujerar Ministan Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa dalilin da ya janyo saukar tsohon Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ba lafiyar sa ba ce kawai, kamar yadda aka bayyana a hukumance, sai dai rikicin cikin gida tsakaninsa da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle. Badaru ya yi murabus ne a ranar 1 ga Disamba bayan matsin lamba da kuma suka da suka yi ƙamari sakamakon tabarbarewar tsaro, hare-haren ‘yan bindiga da kuma sace dalibai da dama a jihohin Arewa. Shugaba Tinubu ya nada tsohon CDS, Janar Christopher Musa (rtd), a matsayin sabon Ministan Tsaro.
Binciken da Jarida Punch ta gudanar ya gano cewa rikici tsakanin Badaru da Matawalle ya daɗe yana ci gaba a bayan fage, duk da cewa suna bayyana suna aiki tare a bainar jama’a. Majiya daga ma’aikatar ta tabbatar da cewa rashin jituwar tasu ya shafi ayyukan ma’aikatar, musamman yadda ake gudanar da hulɗa da kafafen yaɗa labarai. Magoya bayan APC sun fi ganin Matawalle a matsayin ginshiƙi ga zaben 2027, musamman a yankin Arewa maso Yamma, abin da ya sa ya fi samun goyon bayan fadar shugaban kasa fiye da Badaru, wanda ake ganin bai da ƙarfin siyasa a halin yanzu.
Kakaki24 ta kuma gano cewa bayan murabus ɗin Badaru, jama’a da wasu masu ruwa da tsaki sun fara kira ga a sauke Matawalle shima, la’akari da tsanani da matsalar tsaro ta kai. Domin tun shekarar 2024 ake zargin Matawalle da alaka da ‘yan bindiga, duk da cewa ya sha musanta hakan. Har ila yau, kungiyoyin rajin gaskiya da adalci sun yi kira da a kori ministan saboda gazawar da suke ganin tana ci gaba da faruwa a bangaren tsaro. Sai dai majiyoyi a fadar gwamnati sun ce zai ci gaba da rike mukaminsa saboda tasirin sa da kuma rawar da yake takawa a wasu ayyukan binciko ‘yan bindiga, musamman bayan sace dalibai a Kebbi.
A lokacin karɓar aiki, sabon Ministan Tsaro, Janar Musa, ya sha alwashin sake duba dukkan rundunonin yakar ta’addanci a fadin ƙasar, tare da sauya tsarin aiki don inganta haɗin kai tsakanin rundunoni. Ya jaddada cewa jin daɗin sojoji zai zama fifiko, ciki har da biyan alawus a kan lokaci, kayan aiki, da tallafi ga iyalan wadanda suka rasu. Musa ya yi gargadin cewa ba za a yarda da rashawa, sakaci ko karya hakkin dan Adam ba, kana ya ce Najeriya ba za ta iya ci gaba da aikin tsaro da ba su da haɗin kai ba. Ya sha alwashin kawo gyara na gaskiya da na zahiri domin dawo da zaman lafiya da amincin da ‘yan Najeriya ke nema.
